2023: Kungiyar Matasan Daura Sun Nuna Goyan Bayan Bukola Saraki da ya Fito Takarar Shugaban Kasa

 

An kaddamar da kungiyar matasa masu goyon bayan Bukola Saraki ya yi takarar shugaban kasa a 2023.

Abubakar Nuhu Adam, shugaban kungiyar ya ce suna goyon bayan Saraki ne saboda irin ayyukan da ya yi wa matasa.

Adam ya kuma ce ya zabi kaddamar da kungiyar a Daura ne saboda nan ne garinsa kuma don nuna wa duniya rashin jin dadin halin da kasar ke ciki.

Wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar ‘Not Too Young To Run’ da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam’iyyar PDP da wasu sauransu.

“Mun yanke shawarar cewa za mu goyi bayan wanda ke son cigaban matasa kuma Sanata Saraki ne kadai ya cika wannan ka’idar.

“Dukkanmu mun san rawar da ya taka don ganin an aiwatar da dokar Not Too Young To Run a Majalisar Tarayya a lokacin yana shugaban majalisa.

“Mun kuma san cewa shine kadai mamba na kwamitin zartarwa na kasa na PDP da dage cewa dole jam’iyyar ta tallafawa matasa sannan ya goyi bayan matasa su iya yin takara a jam’iyyar,” in ji shi.

Hon Adam ya kuma ce tsohon gwamnan na jahar Kwara ya dauki nauyin dubban matasa domin su kara karatu a jami’o’i daban-daban a duniya. Kazalika, shugaban kungiyar ya ce sun zabi kaddamar da kungiyar a Daura ne saboda nan ne karamar hukumarsa kuma domin su nuna wa duniya rashin gamsuwarsu da halin da kasar ke ciki yanzu.

Daura ce garin Shugaban Nigeria mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here