Ziyarar Tinubu Zuwa Katsina Duk Siyasa ce, ba ta da Wata Alaka da Taimakon Jama’a – Omoluabi Coalition
Wata kungiya a kudu maso yamma ba ta yi farin ciki da matakan Asiwaju Bola Tinubu na kwanan nan ba.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da tallafin da Tinubu ya bayar kwanan nan ga wadanda gobara ta shafa a Katsina, tana mai cewa duk na ganin ido ne kawai.
A cewar kungiyar, wannan ba shine karo na farko da shugaban APC din ke cin amanar mutanensa ba domin neman saukakar siyasa a arewacin Najeriya.
Wata kungiyar kudu maso yamma, Omoluabi Coalition ta yi Allah wadai da ziyara da gudummawar da tsohon gwamnan jahar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya bayar ga wadanda gobara ta shafa a wata kasuwa a jahar Katsina.
Read Also:
A cewar wata sanarwa da kungiyar ta aika wa Legit.ng a ranar Alhamis, 25 ga Maris, kuma da sa hannun shugabanta, Seye Karounwi, tace matakin da jigon na APC ya dauka duk na ganin ido ne kawai.
Wani bangare na sanarwar ya ce:
“Asiwaju Tinubu ya kawar da kai daga irin wannan rikicin a Kasuwar Sasha da ke Ibadan, jahar Oyo ko kuma gobarar da ta tashi kwanan nan a Kasuwar Akesan da ke cikin garin na Oyo, amma ya yi tsalle zuwa jahar Katsina.don tausayawa wadanda lamarin ya rutsa da su kuma ya zama mai kula da’ yan’uwansa.
“Mun yanke shawarar cewa manufar ziyarar Asiwaju Tinubu zuwa Katsina duk siyasa ce, kuma ba ta da wata alaka da taimakon jama’a.”
A baya mun ji cewa Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ya caccaki babban jigo a jam’iyyar All Progressives Congress APC, Bola Tinubu, kan ziyarar da ya kaiwa wadanda gobara ta yiwa illa a Katsina.
Omokri ya yi Alla-wadai da Tinubu kan yadda ya tsallake mutanen da gobara ta lashe dukiyansu a kasuwannin kudu maso yamma amma ya baiwa na Katsina gudunmuwar N50m.