Tinubu ya Taƙaita Yawan Motocin da Ministoci ke Amfani da su a Tawagarsu Zuwa Guda 3
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taƙaita yawan motocin da ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati ke amfani da su a tawagarsu zuwa guda uku, inda ya ce ba za a ƙarawa kowa ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya ce wannan wani mataki daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka na rage kashe kuɗaɗen gwamnati.
Read Also:
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya kuma bai wa ministocin nasa da shugabannin hukumomi da ka da su yi amfani da masu kare lafiyarsu ko jami’an tsaro da suka wuce biyar, inda kuma ya umarci mai bai wa shugaban shawara kan tsaron ƙasa domin tattaunawa da sojoji da ƴansanda da sauran masu ɗamara kan yadda za a rage yawan jami’an tsaron.
Da ma dai ko a watan Janairu sai da shugaban ya ce ya ɗauki matakan rage kashe kuɗaɗen inda ya rage yawan ƴan tawagarsa yayin bulaguro ƙasar waje daga 50 zuwa 20 sannan shi kuma mataimakin shugaban ƙasa aka bar masa mutum biyar.