Shugaba Tinubu ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli Kan Ƙananan Hukumomi
Shugaba Bola Tinubu ya yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke na bayar da cikakken ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi.
Shugaban ya kara da cewa a yanzu kudin kananan hukumomi zai koma karkashin ciyamomi, inda ya ce jama’a za su rika sa ido kan hakan.
Tinubu ya yi imanin cewa rashin ingantaccen tsarin gudanar da kananan hukumomi ne ya kawo cikas ga ci gaban Najeriya, kuma yanzu ya rage ga ciyamomi su yi ayyukan cigaba ga jama’arsu.
Read Also:
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale ya fitar, jim kadan bayan yanke hukuncin a ranar Alhamis, wadda Dayo Olusegun ya wallafa a X.
Tinubu ya bayyana dalilin zuwa kotu
A cewar sanarwar, shugaban ya shigar da karar tun farko ne domin tabbatar da cewa zababbun shugabannin kananan hukumomi ne kawai suke da ikon dukiyar al’umma domin kawo sauki.
Ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta bayyana abin da aka aika a asusun kananan hukumomi, kuma jama’a za su yi wa ciyamominsu alkalanci kan gudanar da ayyuka.
Tinubu ya yi nuni da cewa barnatar da kudin kananan hukumomi da ake yi ya kawo cikas wajen samar da ababen more rayuwa da suka hada da gine-ginen tituna, tsaro, dasaukin rayuwa.