Kungiyar Kiristoci ta Kalubalanci Tinubu da ya Bayyana Sunayen Limaman da Suka Halarcin Taron Gabatar da Shettima

Ana ci gaba da samun takaddama kan manyan limaman coci da aka gani a wajen taron gabatar da Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC.

Kungiyar Kiristoci ta CCCN ta kalubalanci Bola Tinubu da ya bayyana sunayen limaman da suka halarci taron gabatar da Shettima don tabbatar da ingancinsu.

Kiristoci a kasar na adawa da hukuncin APC da Tinubu na yin tikitin yan takara Musulmi da Musulmi a babban zaben kasar mai zuwa.

Mambobin Kungiyar Kiristoci ta CCCN sun zargi jam’iyyar All Progresssives Congress (APC) da tara gayyar malaman addini na bogi,a wajen gabatar da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Kan haka, kungiyar ta CCCN ta kalubalanci jam’iyyar da ta bayyana sunayen fastocin da cocinansu, domin a tabbatar da ingancinsu ko akasin haka, New Telegraph ta rahoto.

Jama’a sun cika da mamaki da ganin manyan Bishop-Bishop da fastoci jere a filin taron gabatar da mataimakin Shugaban kasar na APC a Abuja.

Ana ganin an yi hakan ne domin nuna wa duniya cewa wasu kiristoci na goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi na APC.

Duk da haka, kungiyar ta jaddada cewa tikitin Musulmi da Musulmi bai nuna bambancin ra’ayi da rashin zaman lafiya a kasar.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Rev Bitrus Chollom da sakatarenta na kasa, Fasto James Alkali, kungiyar kiristocin ta yi gargadin cewa hukunci mai tsanani na jiran wadanda suke kokarin muzanta addinin.

Ta kuma sha alwashin bayyanawa duniya sunayen wadanda ke da hannu a lamarin, da nufin fallasa duk abubuwan da suka faru a taron.

Kungiyar ta ce:

“Muna kalubalantar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya bayyanawa duniya sunayen fastoci da manyan Bishop-Bishop, wadanda basu yarda da kansu ba saboda abun da ya wakana a taron.

“Ga dukkanin wadanda abun ya shafa, muna shawartanku da ku tuba, ku yi tir da abubuwan da suka kulla taron, don hakan ya zama gyara.”

Tun da farko, kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta kalubalanci jam’iyyar APC mai mulki da ta bayyana sunayen malamanta da aka ce sun halarci taron kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here