Shugaban Amurka Donald Trump ya Rungumi  Qaddara

Bayan an kai ruwa rana, shugaba Trump na kasar Amurka ya yarda cewa Sanata Joe Biden ya kayar da shi.

Trump ya ki yarda cewa Sanata Biden ya kayar da shi duk da sakamakon zabe ya nuna hakan.

Tun kafin a gudanar da zabe Trump ya ki amsa tambayar ko zai mika mulki idan ya fadi zaben kujerar shugaban kasa a Amurka.

A karshe, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince cewa ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa, Sanata Joe Biden.

A wani sako da ya wallafa ranar Lahadi, Trump ya yarda Biden ya samu nasara amma ta hanyar tafka magudin zabe.

“Ya samu nasara ne saboda an tafka magudi a zaben. Babu masu sa-ido, babu masu lura da zabe. An yi amfani da wani kamfani da sunansa ya gurbata wajen tattara sakamakon zabe. Kafafen yada labarai da ke yada labaran bogi, da wadanda suka yi shiru, suka ki yin magana, duk sun taimaka wajen danne nasarar da na samu a Texas,” kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Trump ya yi ikirarin samun nasara a daren da aka kammala zaben shugaban kasar Amurka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here