Dakarun Sojojin Najeriya Sun Kashe Wasu ‘Yan Boko Haram Sun Kama Mai Hada Bama-Bamai

Dakarun sojin Najeriya suna samun manyan nasarori a yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

A wani samame na musamman da dakarun suka kai, sun samu nasarar halaka mayakan ta’addancin masu tarin yawa.

Sojojin sun samu nasarar damke kwararru wurin hada bama-bamai wadanda mayakan ke amfani da su.

Samamen da dakarun sojin kasar nan ke cigaba da kaiwa yana matukar tasiri a yankin arewa maso gabas na kasar nan. Sun yi nasarar damke wasu masu hada bama-bamai.

Wannan nasarar na kunshe ne wata takardar da hedkwatar tsaro ta kasa ta fitar a ranar Lahadi wacce Birgediya Janar Benard Onyeuko yasa hannu.

Ya ce da yawa daga cikin mayakan ta’addancin sun sheka lahira bayan samame da ruwan wutan da rundunar Opertaion Lafiya Dole suka musu.

Kamar yadda takardar ta fitar, rundunar dakarun sojin sun samu wannan nasarar ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2020.

Bataliya ta 151 ta sojoji na musamman da ke yankin Miyanti sun yi aiki da bayanan sirri inda suka tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan da ke kauyen ladantar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here