APC ta Rasa Daya Daga Cikin Manyan Jiga-Jiganta – Samuel Ojebode

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa wani babban jigonta, Samuel Ojebode, a Oyo.

Ojebode, ya kasance Shugaban jam’iyyar a mazabar tarayya ta Oyo.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar sun nuna alhininsu kan mutuwar Ojebode.

Abun bakin ciki da alhini ya samu jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayinda ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta, Samuel Ojebode.

Ojebode, wanda ya kasance jigon APC a jihar Oyo, ya rasu a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, yana da shekaru 87 a duniya.

A wani sakon ta’aziyya, wani sanata daga jihar, Teslim Folarin, ya nuna bakin cikinsa.

A wani jawabi daga Yakeeen Olaniyi a Ibadan, Folarin ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban asara ga ahlin APC a Najeriya.

Folarin ya tuna cewa jigon na APC ya shirya taro na lumana mai cike da nasara ga mambobin jam’iyyar a mazabar Oyo ta tarayya.

Ya ce Ojebode ya kasance shugaba abun koyi, mai mutunci da kima.

A sakon ta’aziyyarsa, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Farfesa Adeolu Akande, Shugaban hukumar NCC, ya yi ta’aziyya ga iyalai, abokai da mambobin APC a jihar kan wannan rashi.

A cewar Akande, Ojebode ya kasance dan siyasa na hakika kuma shugaba daba a cika samun irinsa ba sannan cewa za a yi kewarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here