Amurka: Trump ya ki Amincewa da Nasarar Biden

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai amince da nasarar da ake ganin abokin hammayarsa Joe Biden ya samu ba.

Trump ya ce ba kafafen watsa labarai ne ke sanar da wanda ya lashe zabe ba don haka har yanzu ba a gama zabe ba.

Har wa yau, Trump ya yi ikirarin cewa akwai matsala tattare da zaben inda ya ce an hana wakilan jam’iyyarsa masu saka ido shiga wurin kirga kuri’u a Pennsylvania Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ki amincewa da nasarar zabebben shugaba Joe Biden.

Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter jim kadan bayan da kafafen watsa labarai suka ambaton nasarar tsohon mataimakin shugaban kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Dan takarar na jam’iyyar Republican Party ya ce an tafka kure-kurai da dama a zaben don haka zai garzaya kotu a ranar Litinin don kallubalantar sakamakon zaben.

Ya ce, “Dukkan mu mun san dalilin da yasa Joe Biden ke gaggawan nuna kansa a matsayin wanda ya yi nasara, da kuma dalilin da yasa abokansa na kafafen watsa labarai ko kokarin ganin sun taimaka masa: Ba su son gaskiya ta bayyana.

Maganar gaskiya ita ce har yanzu ba a gama zabe ba.

” Trump ya ce ba a tabbatar da Biden a matsayin dan takarar da ya lashe zabe a ko jiha guda ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here