Yadda na Tsallake Rijiya da Baya a Harin ‘Yan Bindiga – Tsohon Kwamishinan Mahalli na Jihar Nasarawa

 

Nasarawa – Kwamishinan muhalli da ma’adanai da bai jima da sauka daga muƙaminsa ba a jihar Nasarawa, Musa Ibrahim Abubakar, ya tsallake rijiya da baya a harin ‘yan bindiga.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a baya-bayan nan Mista Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani na fidda yan takarar majalisar jiha.

Bayan ficewa daga APC, tsohon kwamishinan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari inda ya karɓi tikitin takarar mamba mai wakiltar mazaɓar Dama ta kudu a majalisar dokokin Nasarawa.

Da yake labarta yadda ya tsallake harin ga yan jarida yayin da yake jinya a Asibiti, Abubakar yace:

“Ina cikin raɗaɗi, amma ina son bayyana wa duniya cewa a ranar 21 ga wannan watan, na je garin Rukubi na raba kayan tallafi da suka haɗa da tsabar kuɗi ga mutanen da Ibtila’in ambaliya ta shafa a ƙaramar hukumata, Doma.”

“Bayan gama aikin, na kama hanyar komawa gida a garin Doma, ba zato wasu ‘yan bindiga kusan 9 suka buɗe mun wuta ta kowane ɓangare. Harsashi ya same ni ta gaba wayar salula ta kare, wani ya same ni a kafaɗa da baya na.”

“Harsasai 46 aka harbi motata da su, lamarin ya faru da karfe 5:30 na yamma a kusa da ƙauyen Igbabo, kusan kilo mita 20 zuwa garin Doma. Ina da yaƙinin waɗanda suka farmake ni manyan yan siyasa ne a wata jam’iyya.”

Ta ya tsohon kwamishinan ya tsira?

Da yake ƙara bayani kan lamarin, tsohon kwamishinan yace lokacin maharan masu nufin kashe shi ke cigaba da harbi sai ya ƙara gudu da motarsa a kokarin tsere musu.

Yace yana cikin tafiya kawai motar ta tsaya yana gab da shiga ƙauyen Igbabo, daga nan ya samu ya fice da gudu yana kuruwar neman taimakon mutane.

A cewarsa, wasu mutanen kirki suka taimaka suka ɗauke shi a Babur zuwa garin Doma, daga nan ya wuce Asibirin Ɗalhatu Araf Special Hospital dake Lafiya, babban birnin jihar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here