Dole Kowanne ‘Dan Takara ya bi Tsari Wajen Neman Takara, ko da Kuwa Jonathan ne a Zaben 2023 – APC

 

Jam’iyyar APC da ke mulkin Najeriya ta ce babu wani mamba cikin sabbin mutanen da suka koma jam’iyyar da za a bawa tiketin takara kai-tsaye, ko da kuwa Goodluck Jonathan ne a zaben 2023.

A wata sanarwa da suka fitar ranar Juma’a, sakataren kwamitin riko na jam’iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe ya ce tattaunawarsa da Talabijin Channels a ranar Laraba ba ta shaida cewa za a bawa Jonathan takara kai-tsaye ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa dukkanin mambobin jam’iyyar za su samu gajiya da damamaki da kowa zai samu.

APC ta kuma ce dole kowanne dan takara ya bi tsari wajen neman takara da amincewa jam’iyyar ta tsayar da shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here