Babban Bankin Najeriya ya na Neman Mai Shafin Canji na AbokiFX

 

Babban bankin Najeriya wato CBN ya ce yana neman mai shafin canji na AbokiFX, Oniwinde Adedotun ruwa a Jallo.

AbokiFX shafin ne da ke wallafa bayanai kan yanayin hada-hada da yada ake sauya kudaden ketare akan naira a kasuwanni bayan-fagge.

A lokacin da ya ke amsa tambayoyi a taron manufofin kudi karo na 280 a hedikwatar bankin da ke Abuja, gwamnan Bankin Godwin Emefiele ya ce mai shafin AbokiFX na gudanar da harkokinsa ta haramtacciyar hanya.

Ya ce za a gurfanar da shi kan jefa tattalin arzikin Najeriya cikin barazana.

A cewar gwamna Emefiele, Mista Oniwinde ya soma shafin AbokiFX a 2015, kuma tun daga wannan lokaci ya ke zagon-kasa ga tattalin arzikin kasa ta hanyar amfani da shafin ta mumunar hanya.

”Oniwinde tun daga inda ya ke rayuwa wato Landan, ya ke aikata muggan laifuka ga tattalin arzikinmu.”

A cewar Godwin CBN kadai ke da damar yanke hukunci kan darajar Naira, don haka ya sha alwashin kamo Oniwinde domin fuskantar shari’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here