Yajin Aikin NARD: Likitoci Sun yi Alla-Wadai da Hukuncin Kotun Ma’aikatan NIC Kan Cewa su Koma Bakin Aiki

 

Likitoci sun yi martani kan hukuncin kotun ma’aikatan NIC.

Likitocin sun fara yajin aiki ne ranar 1 ga Agusta bisa rashin biyansu albashi da kuma sauran wasu dalilai.

Alkalin kotun yace mutane zasu cigaba da mutuwa idan Likitoci basu koma aiki ba.

Abuja – Shugabannin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya NARD sun yi Alla-wadai da hukuncin kotun ma’aikatan Najeriya da ta umurci mambobinta su koma bakin aiki.

A takardar da Shugaban kungiyar, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, da Sakataren kungiya Dr Jerry Isogun, suka saki ranar Juma’a. sun bayyana cewa sun fara daukaka kara.

Jawabin yace:

“Kamar yadda muka sani, musamman wadanda ke kotu yau, kotu yau… Bamu gamsu da hukuncin kotu ba.”

“Bayan tattaunawa da Lauyoyinmu, mun umurcesu su daukaka kara kuma su nemi a dakatad da aiwatar da umurnin kotun.”

Shin zasu koma aiki ne?

Maimakon umurtan mambobinta su koma bakin aiki, kungiyar Likitocin tace lauyoyinta su koma kotu.

Hakazalika ta umurci mambobin su kwantar da hankulansu.

Suka ce:

“Muna kan bakanmu na cigaba da kare hakkinku. Mun yi imanin zamu samu nasara.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here