Magance Tsaro: Jahar Katsina ta Fitar da Sabon Tsarin Fentin Ababen Hawa na Haya a Jahar
Gwamnatin Katsina ta fitar da sabon tsarin kalolin fentin motocin haya a jahar.
Wannan na daga cikin matakan tabbatar da tsaro da gwamnatin ke dauka, cewar kwamishanan sufuri.
Wannan ya biyo bayan dokar hana hawa ababen hawa a wasu garuruwa.
Katsina – Gwamnatin Jahar Katsina ta fitar da samfurin sabbin kalolin fentin da ake son masu ababen hawan haya suyi wa motoci da kurkurorinsu (Keke Napep).
Majalisar zartarwar jahar Katsina ta amince da wannan sabon tsari ne a zaman da tayi na karshe a dakin taro na Gidan Janar Muhammadu Buhari.
Majalisar ta amince da irin kalolin fentin da za a yiwa ababen hawan.
Kalolin dai sune kalar dorowa da kuma kalar bula.
Read Also:
Bayan haka, za’a fitar da tsarin sanyawa kowace mota lamba ta musamman da za ta banbancesu bisa kananan hukumomin da suka fito.
Kwamishinan Ayyuka da gidaje na jahar Katsina ya bayyana hakan a yayin zama da akayi da manema labarai, rahoton Katsina Post.
Ya kara cewa hakan duk yana cikin kokarin tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar jahar nan.
A rika lura da sa ido kan masu kaiwa yan bindiga bayanai
Haka kuma, gwamnatin jahar ta ja hankalin al’umma da suka sa ido sosai wajen gano bata garin cikin mu da suke aike ma ‘yan ta’adda da bayanai domin hadarin su yafi na masu ta’addancin.
Mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya bada tabbacin cewa ba za’a daina aikin da aka fara a kananan hukumomin Jibia da Batsari ba sai an tabbatar da an kakkabe ‘yan ta’addar da suka addabi al’umma.