Shugaba Buhari ya Bayyana Abinda Yake ba shi Mamaki da ‘Yan Kabilar Igbo

 

Buhari ya samu muhimman karramawa daga wajen shugabannin yankin Igbo.

Shugaban kasan ya kai ziyara jahar Imo ranar Alhamis, 9 ga Satumba.

Buhari yace yana mamakin dalilin da zai sa yan kabilar su rika tunanin ballewa daga Najeriya.

Imo – Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kabilar Igbo a matsayin wadanda ke rike da akalar tattalin arzikin Najeriya saboda haka yana mamaki ace suna son ballewa.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyarar kaddamar da titunan da aka kammala a jahar Imo karkashin gwamna Hope Uzodinma na jahar.

Yace abu mafi muhimmancin ga Ƴan kabilar Ibo Shine, babu wani gari dazaka ziyarta a Najeriya ba tare da ganin Dan kabilar Ibo wa lau jagora akan abun more rayuwa ko kamfanin samar da magani.

Buhari yace:

“A saboda haka, abinda mamaki ne gare ni cewa Dan Kabilar Ibo ya dauki kanshi cewa shi ba wani sashe na Najeriya ne ba.

“Hujjoji na Nan fa kowa don su gani cewa Dan kabilar Ibo suke Manyan jagorori a tattalin arzikin Najeriya.”

Buhari ya kara da cewa babu wata kasa da zata samu wani cigaban azo a gani ba tare da samun manyan aiyukan gina ƙasa ba.

Hakazalika, Ya yi Alkawari cewa, Gwamnatin Tarayya zata kammala aiyukan da take aikatawa a yankin Kudu maso Gabas, ciki harda Babbar Gada na (2nd Niger Bridge) dama kuma layin dogo daya kara de da hada Shiyar da Sauran sassan Kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here