Zamu Saka Tsauraran Matakai Kan Wanda Basu yi Rigakafin Corona ba – Gwamatin Jahar Edo

 

Gwamnatin jahar Edo ta bayyana cewa dole ne maazauna jahar su yi riga-kafin corona ko kuma ta bullo musu ta bayan gida.

Gwamnan jahar, Godwin Obaseki ya ce za a hana shiga masallatai, majami’u da bankuna ba tare da shaidar yin riga-kafin ba.

Kamar yadda ya shaida, tarukan shagulgulan biki za su haramta ga duk wanda bashi da shaidar yin riga-kafin muguwar cutar.

Benin City, Edo – Gwamnatin jahar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami’u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta rawaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jahar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar corona a Benin City.

Bayanin Obaseki kan matakin da zai dauka Ya ce cutar korona nau’in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama’a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta rawaito.

Muna da nau’ikan riga-kafi biyu, akwai riga-kafin Moderna wanda bamu dade da samu ba, akwai kuma riga-kafin Astrazeneca ga wadanda z asu karba kashi na biyunsu.

A cikin kwanakin karshen makon nan ne jahar Edo ta karba magugunan allurar riga-kafi 76,712, wanda ya hada da allurai 65,016 na Moderna da 11,696 na AstraZeneca.

Kamar yadda yace, gwamnati ba za ta rufe jahar ba amma za ta baiwa rayukan jama’a kariya. Ya kara da cewa daga watan Satumba, za a haramta shiga taro mai mutane da yawa ga wadanda basu karba riga-kafin cutar ba.

Daga mako na biyu na watan Satumba, ba za a bar jama’a su shiga majami’u, masallatai, wuraren shagulgulan biki, liyafofi da kuma wuraren cin abinci ba, ba tare da katin shaidar yin riga-kafin ba.

Hakazalika, daga mako na biyu na watan Satumba, ba za a bar jama’a su dinga shiga bankuna ba, ba tare da katin shaidar yin riga-kafin cutar corona ba. Don haka duk wanda yake son walwala, yayi riga-kafi kawai.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here