Dalilin da Yasa Gwamnatin Buhari ta Saka Tsauri Wajen Ka’idojin Tafiye-Tafiye

 

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri wajen ka’idojin tafiye-tafiye.

Gwamnatin ta ce wannan ba komai bane face nema wa ‘yan kasar sauki wajen kare kansu.

Gwamnatin ta kuma ce, ta ware wasu kasashe da tace su ne kasashe masu hadarin gaske

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta ce ta sanya tsauraran ka’idojin balaguro zuwa kasashen waje ne don kare ‘yan kasar daga kamuwa da cutar ta corona, Punch ta ruwaito.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Laraba 11 ga awatan Agusta.

Mohammed ya ce an sanya Najeriya a matsayin kasa mai tsaurin ra’ayi dangane da ka’idojin tafiye-tafiye, yana mai bayanin cewa matsayin gwamnati shi ne kare mutanenta daga yaduwar cutar.

A cewarsa:

“An zarge mu da cewa dokokin mu suna da tsauri. Mun ce a’a. Ba mu kasance masu tauri saboda taurin kai ba. Muna da tauri ne saboda abin da kimiyya ke bukata. Muna da tsauri ne saboda muna son kare mutanen mu.

Ministan ya bayyana cewa, Najeriya ta sanya wasu kasashe ne a jerin kasashe masu hadari kasancewar bullar annobar Korona nau’in Delta.

“Mun sanya musu suna kebabbun kasashe da aka sanya wa takunkumi. Ya zuwa yau, muna da guda hudu kadai irin wannan; Afirka ta Kudu, Indiya, Brazil da Turkiya.

“Kuma akwai tsauraran ka’idojin balaguro a kan wadannan kasashe saboda muna son hanawa da kare mutanenmu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here