An Tsinci Gawar Farfesa na Jami’ar UNICAL
An tsinci gawar Farfesa a fannin kwas ɗin kimiyyar siyasa, Farfesa Felix Akpan, na jami’ar Kalaba (UNICAL).
Kakakin yan sanda a jihar Kuros Riba, ya ce tuni suka kama wani abokinsa da ake zargi, suna kan bincike.
Wata majiya daga Anguwar da lamarin ya faru ta bayyana yadda abun ya afku tun daga farko.
Cross River – Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kuros Riba ta tabbatar da gano gawar wani Farfesan Kimiyyar siyasa daga jami’ar Kalaba, Farfesa Felix Akpan.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an tsinci gawar ne ranar Lahadi.
A cewarsa, an gano gawar ɗauke da raunukan burma wuka a wurare da dama a gidan mamacin da ke Plot 181, garin Duke kusa da rukunin gidajen jiha a Kalaba.
Mista Ugbo ya ce sun fara kama waɗanda ake zargi da hannu yayin da jami’ai suka buɗe shafin bincike kan kisan, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Kakakin yan sandan ya ce:
Read Also:
“Akwai wanda ake zargi tsare a hannun mu, wanda ya yi ikirarin abokin mamacin ne (Farfesa Akpan), ya ce bai san abinda ya faru ba ko wanda ya soka masa wuka har ya mutu.”
“Tuni tawagar bin diddigi suka fara aiki, nan ba da jimawa ba zamu tono tushen lamarin ta hanyar gano asalin wanda ya aikata kisan.”
Akwai wanda ake zargi – Majiya
Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta, ta ce mamacin, tsohon shugaban sashin kula da jin daɗin daliban jami’ar UNICAL ya yi wani baƙo ranar Asabar.
Baƙon ya tafi da sanyin safiyar ranar Lahadi zuwa Akampka kafin daga bisani a gano gawar farfesan.
NAN ta rahoto majiyar na cewa:
“Ya yi wani baƙo namiji, wanda ya zo masa ziyara a ƙarshen mako, amma mutumin ya tafi da sanyin safiyar Lahadi kamar karfe 5:00 na Asuba.”
“Wata da ke zama a Anguwa ta ce ta ji ƙara daga gidan a wannan rana da wannan baƙon, wanda aka tabbatar abokinsa ne, ya bar gidan kuma ta yi hanzarin faɗawa makota ƙarar da ta jiyo.”
“Bisa sa’a bakon ya manta wani abu da ya sa ya dawo gidan domin ya ɗauka, daga nan aka cafke shi, muka tafi da shi gidan Farfesa Akpan, inda muka gano gawarsa da tabon soka wuka.”