Tsofaffin Kudi: Gwamnatin Delta ta Roki ‘Yan Jihar su bi Umarnin CBN

 

Gwamnatin jihar Delta karkashin abokin takarar Atiku ta roki ‘yan jihar su bi umarnin babban banki CBN.

Kwamishinan yaɗa labarai ya ce gwamnatin ba ta da masaniyar wahalar da mutane suka sha sanadin sauya naira.

Ya roki yan kasuwa, gidajen mai, masu karban harajin gwamnati da sauransu su karbi tsohon naira.

Delta – Gwamnatin jihar Delta karkashin jagorancin gwamna Ifeanyi Okowa ta roki mazauna jihar su yi biyayya ga umarnin babban bankin Najeriya (CBN).

Punch ta tattaro cewa CBN ya umarci ‘yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Delta, Mista Charles Aniagwu ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya fitar a Asaba, babban birnin jiha.

Ya roki mazauna jihar da su ci gaba da harkokin gabansu da tsoffin takardun kuɗin duba da hukuncin Kotun koli da CBN, wanda ya tsawaita halascin amfani da takardun.

Haka nan ya yi kira ga ma’aikatan da ke tattara harajin gwamnati, gidajen mai, masu Tireda, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki su bi umarnin CBN.

Bamu san mutane sun shiga wahala ba – Gwamnatin Delta

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Delta ba ta san sabon tsarin sauya fasalin naira ya jefa mutane cikin ƙaƙanikayi da wahalhalun rayuwa ba.

Amma duk da haka, Mista Aniagwu ya bukaci mazauna su yi amfani da wannan damar da hukuncin Kotun koli ya samar musu, su rage raɗaɗi da kuncin da tsarin ya haifar masu.

Vanguard ta ce daga nan ya yi kira ga dukkan hukumomin gwamnatin Dele masu alhaki da sauran masu ruwa da tsaki da su karbi tsohon kuɗi daga hannun mutane.

“Muna shawartan hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki, kar su ki karban tsohon kuɗi idan mutane sun yi amfani da su wajen biyan wani haƙƙi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here