INEC za ta bai wa Jam’iyyun PDP da LP Damar Duba Kayan Zaɓen shugaban ƙasa

 

Hukumar zaɓen Najeriya, ta yi alƙawarin miƙa dukkanin kayan zaɓen da ƴan hamayya za su buƙata waɗanda aka yi amfani da su a zaɓen watan da ya gabata na shugaban ƙasa ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Shugaban na INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, hukumar ba ta da wani abu da za ta ɓoye a zaɓen da ake taƙaddama a kansa.

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kuma ta Labour (LP), suna son duba kayan zaɓen ne domin su samu damar shirya wa ƙarar da za su shigar ta ƙalubalantar sakamakon zaɓen, wanda INEC ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, a matsayin wanda ya yi nasara.

Jam’iyyun suna da mako biyu ne kawai su shigar da ƙara.

Jam’iyyar Labour ta yi barazanar shirya zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya idan INEC ta hana ta duba kayayyakin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here