Tsohuwar Ministar kuɗin Najeriya na dab da Zama Shugabar WTO
Jekadun kasashe a ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya WTO sun gabatar da sunan tsohuwar ministar kuɗin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar.
Idan dai har aka zaɓi Ngozi Okonjo-Iweala, za ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da ta taba riƙe mukamin a tarihin ƙungiyar.
Ngozi ta samu goyon bayan jakadun ƙasashe, Haka ma ta samu goyon bayan Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka.
Ngozi na fafata wa ne da Ministar Kasuwanci ta Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee a zagayen ƙarshe na takarar kujerar shugabancin Ƙungiyar.
Ƙasar Amurka na adawa da zaɓen Okonjo-Iweala, inda ta ke goyon bayan ƴan takara daga Koriya Ta Kudu Yoo Myung-hee.
Wani rukuni na jakadun ƙasashe mambobin ƙungiyar ne suka fitar da sunan Ngozi sannan suka shaida wa sauran mambobi.
Wannan ya biyo bayan wata ganawa da Babban Zauren WTO ya yi ne danar Laraba a Geneva, babban birnin ƙasar Switzerland.
Akwai Ƙalubale
Ƙungiyar WTO na fatan cimma matsaya kan zaɓin sabon shugaba. Kuma dole sai an samu jituwa kafin zaben sabon shugaban ƙungiyar.
Ƙasashe da dama ne suka yi gwagwarmayar ganin an naɗa Ngozi domin jagorantar muhimmiyar ƙungiyar kasuwanci ta duniya mai mambobi 164.
Mai Magana da yawun WTO ya ce za a gabatar da takararta ga babban zauren ƙungiyar ranar 9 ga Nuwamba don amincewa da jagorancinta, amma akwai yiwuwar fuskantar ƙalubale kafin tabbatar da yarjejeniyar da ake bukata.
Dakta Ngozi Okonjo-Iweala tana da ƙwarewa ta sama da shekaru 30 kan tattalin arziki da ci gaba, inda ta yi aiki a Afirka da Asiya da Turai da Latin Amurka.
Nagozi ta yi aiki a Bankin Duniya tsawon shekara 25 kafin zama ministar ƙudi a Najeriya.
Najeriya ta bayyana farin cikinta da yadda galibin kasashe suka nuna goyon baya ga Ngozi Okonjo-Iweala domin jagorantar kungiyar mai sa ido kan harkokin cinikayya a duniya.