Ibadan: Dalibai Na Fuskantar Tsangwama, an Saka Wuta a Ofishin Shugaban Makarantar

Har yanzu, dalibai basu daina fuskantar tsangwama kan irin tufafin da suke sanyawa ba

Yayinda ake hana wasu shiga don sun sanya Hijabi, ana hana wasu shiga don bayyana tsiraici An samu tashin hankali a garin Machinga dake kasar Malawi inda wasu matasa suka bankawa ofishin shugaban makarantar firamare wuta.

Matasan sun aikata hakan ne don shugaban makarantan ya hana dalibai masu Hijabi shiga aji, BBC Hausa ta ruwaito. Wannan abu ya faru ne a makarantan firamaren Mpiri mallakar cocin Katolika. Jami’an yan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin kuma sun ce an kone ofishin kurmus. Garin Machinga na da mazauna masu mabanbantan addini musamman Musulmai da Kirista, amma mafi akasarin makarantun garin mallakin Kiristoci ne.

An ruwaito cewa babu wata dokar gwamnati da ta ayyana irin kayan da ɗalibai za su saka, sai dai makarantun kan hana ɗalibai saka hijabi, abin da ke jawo rikici daban-daban. Makarantun sun yi barazanar rufewa saboda tashin hankalin da ke faruwa.  Hankula sun tashi a Ibadan saboda hana dalibai mata sanya Hijabi a makarantar sakandari

Shugabar makarantar da kanta mai suna, Phebean Olowe, ta sallami dalibar.
Diraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, a wani jawabi da ya saki ranar Litinin ya nuna bacin ransa kan wannan abu

Yace: “Ya bayyana karara cewa shugabar makarantar bata iya sulhu ba kuma bata ki abubuwa su tabarbare ba.” “A Turai da Amurka inda Musulmai ba su yawa, an halatta sanya hijabi a makarantu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here