Sanata Omo Agege ya Yaba wa Mutumin da ya Tuƙa Tankar Fetur da ke ci da Wuta ya Fitar da Ita Daga Cikin Mutane a Jihar Delta.
Wani mutumi ya ja hankalin mutane bayan ya nuna rashin tsoro, ya Tuƙa Tankar Fetur da ta kama da wuta ya fitar da ita daga cikin mutane.
Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Omo Agege, ya kira shi ta waya don jinjina masa kan kokarin da ya yi a jihar Delta.
Mutumin wanda dama can Direba ne, ya nuna tsantsar jin daɗinsa da kiran Sanatan, ɗan takarar gwamna na APC.
Delta – Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Omo Agege, ya yaba wa wani direba, Ejiro Otarigho, wanda ya tuƙa Tankar Fetur da ke ci da wuta ya fitar da ita daga cikin mutane a jihar Delta.
A ƙarshen makon nan, wani Bidiyo da aka watsa a Tuwita, ya nuna yadda Otarigho ya tuƙa Tankar mai ci da wuta a ƙauyen Agbarho, jihar Delta.
The Cable ta ce yayin da yake zantawa da mutumin ta wayar salula, Omo-Agege, ɗan takarar gwamnan Delta na APC, ya bayyana mutumin da, “Gwarzo.”
Read Also:
Sanatan ya ce ba don sadaukarwan direban ba, da wata Annobar wuta ta tashi a yankin wacce ba’a san iya ɓarnar rayukan mutane da dukiyoyin da zata yi ba.
Ya ce:
“Aikin da ka yi ya ceci rayukan al’ummar mu waɗan da ka iya mutuwa sanadin hatsarin. Ba kowane mutum zai iya samun irin wannan karfin halin ba, abun da kayin nan ɗaya ya tseratar da Agbarho, muna alfahari da kai.”
“A wurina ka zama gwarzon mutanen mu kuma ina da tabbacin mutane da yawa zasu neme ka yanzu, dan haka lokacin ka ne da zaka ji kai gwarzo ne, ina alfahari da kai.”
Yadda mutumin ya ji bayan kiran Sanatan
A ɓangarensa, Otarigho, ya bayyana cewa kiran da Omo-Agege ya masa ya tabbatar da yanda yake kula da nuna sanayya ga mutane.
“Mutum kamar mataimakin shugaban majalisar Dattawa ya kira ni a irin lokacin nan, na yi matuƙar farin ciki da hakan. Jin ta bakinsa ya nuna yadda yake nuna sanayya ga mutane.”
“Mutane na ƙorafin ba wanda zai kula da su, inda na bar mutane sun mutu sai dai a zo ganin gawarwaki, amma yanzu na ji daɗi mataimakin shugaban majalisa ya kira ni.”