Kotu ta Yankewa Mutane 2 Daga Cikin Abokan Abba Kyari Hukunci

A yau ne wata babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta yankewa biyu daga cikin abokan harkallar Abba Kyari hukunci.

Hakazalika, kotun ta bayyana ranakun da za ta zauna domin sake sauraran batun da ya shafi hukuncin Kyari.

Ana zargin Abba Kyari da wasu mutane ne da laifin safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa a farkon shekarar nan.

Abuja – Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta yanke hukuncin daurin shekaru shida a gidan kaso ga Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwane, wadanda ake alakanta su da DCP Abba Kyari.

Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Emeka Nite ya yanke, ta kama Umeibe da Ezenwanne da laifuka 5, 6 da 7 na laifin safarar miyagun kwayoyi da NDLEA ta fifita a kansu, Vanguard ta ruwaito.

Idan ba ku manta ba a ranar 7 ga watan Maris ne aka gurfanar da mutanen biyu wadanda aka kama a filin jirgin saman Akanu Ibiam na Enugu a lokacin da suke kokarin shigo da hodar iblis Najeriya daga waje.

Hakazalika, a ranar ne aka gurfanar da DCP Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda hudu – ACP Sunday J. Ubia. , Insp. Simon Agirigba, Insp. John Nuhu, da ASP Bawa James.

Duka Umeibe da Ezenwanne sun amsa laifinsu na safarar miyagun kwayoyi da ake tuhumarsu da aikatawa.

Bayan jin batutuwa, kotun ta yanke musu hukunci, inda za su zauna a gidan kaso na tsawon shekaru shida.

Sai dai kotun da ta yi nuni da cewa wadanda ake tuhumar biyu sun yi nadama, ta ce hukuncin zai ci gaba da gudana ne daga ranar da aka kama su.

Bugu da kari, kotun, ta ce wadanda ake tuhumar su miko da fasfo dinsu na kasa da kasa kamar yadda sashe na 30 na dokar NDLEA, Cap M30, dokokin Tarayyar Najeriya ya tanada.

A bangare guda, kotun ta ba Umeibe da Ezenwanne damar ba da shaida a shari’ar DCP Kyari da sauran jami’an ‘yan sanda da ake tuhuma, kana ta umarci hukumar NDLEA da ta tabbatar da tsaron lafiyarsu a duk wani gidan gyaran hali da suke so.

Ta umurci hukumar ta NDLEA da ta ci gaba da sanya ido a kan wadanda ake tuhumar guda biyu don tabbatar da cewa ba su aikata wani laifin da ya shafi miyagun kwayoyi ba yayin da suke zaman gidan yari.

Daga nan ne Mai shari’a Nwite ya sanya ranar 18, 19 da 20 ga watan Yuli domin ci gaba da shari’ar DCP Kyari da mutanensa, da kuma sauraron sabon bukatarsu na neman beli.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here