Ukraine ta Nemi ‘Yan Kasarta da su Rage Yawan Amfani da Wutar Lantarki
Ministan makamashin Ukraine ya ce jama’a sun fara rage yawan wutar lantarki da suke amfani da ita don kashin kansu saboda karancin wutar a fadin kasar.
To amma Herman Halushchenko ya ce duk da haka gwamnati ba ta da zabi face ta ci gaba da dauke wuta lokaci zuwa lokaci saboda karancin.
Read Also:
Ministan ya ce hare-hare sama da 300 da Rasha ta kai musamman a kwanaki 10 da suka wuce sun lalata hanyoyin samar da wutar a garuruwa da dama.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce kashi daya bisa uku na Ukraine ya rasa wutar lantarki saboda hare- haren na Rasha.
Mista Zelensky ya ce ”a ranar Laraba kadai tashoshinmu uku abokan gaba suka lalata, to amma za mu yi duk abin da za mu iya mu ga cewa mun gyara su.
Wakilin BBC a can ya ce an kashe wutar kan titi a wasu wurare, an kuma umarci al’umma su rage amfani da abubuwa da ke jan wuta sosai a gidajensu.