Kotu ta Bayar da Umarnin Kwace Kadarorin Tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

 

Hukumar ICPC mai binciken laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba ta umarni na wucin gadi na kwace wasu kadarorin tsohon Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari.

Kaddarorin sun haɗa da gine-gine da kudaden da tsohon gwamnan ya ajiye a wasu bankunan kasar.

A yau Laraba alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Obiora Egwuatu ta bayar da umarnin kwace kadarorin, ciki har da wasu gine-gine 10 da ke ciki da wajen Najeriya.

Kakakin hukumar Misis Azuka Ogugua ta tabbatar wa BBC Hausa cewa wannan nasarar ta wucin gadi ce, kuma bayan lokacin da kotun ta diba, gwamnatin Najeriya na iya kwace kadarorin idan tsohon gwamnan ya kasa gamsar da kotu cewa ya mallaki su ta halaliyar hanya.

Ta ce: “Abin da wannan ke nufi shi ne bayan lokacin da kotun ta diba, kuma babu wanda ya iya gamsar da shari’a cewa ya mallaki kadarorin ta halattacciyar hanya, kotu za ta mika wa gwamnatin tarayya dukkan kadarorin na dindindin ke nan.”

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan wani hukunci irinsa da wata babbar kotun ta yanke tana bayar da umarnin a kwace kusan naira miliyan 279 ciki har da dalolin Amurka da ta gano tsohon gwamnan ya mallaka ta haramtacciyar hanya.

Wasu cikin kadarorin da aka kwace suna manyan unguwanni a biranen Abuja da Kaduna da Zamfara da jihar Maryland ta Amurka.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here