Wanda Ake Zaton Zai Zama Shugaban Barcelona
Wanda ake tunanin zai zama shugaban Barcelona Victor Font, na son dawo da kocin Manchester City Pep Guardiola. Guardiola ya shiga wa’adin ƙarshe na kwangilar sa a Etihad. (Sky Sports)
Mai tsaron baya a Tottenham Toby Alderweireld na iya barin ƙungiyar da ke buga Firimiya, idan kwantiraginsa ta kare a 2023, a cewar mahaifin ɗan wasan asalin Belgium mai shekara 31. (Teamtalk)
Liverpool har zuwa idon ta na kan Kalidou Koulibaly na Napoli kuma tana iya sake tayin ɗan wasan asalin Senegel mai shekara 19, a watan Janairu. (Calciomercato – in Italian)
Ɗan wasan Lille da ke buga gaba a Amurka Timothy Weah mai shekara 20, na iya koma wa Saint-Etienne a matsayin aro. (L’Equipe – in French)
Tsohon mai tsaron baya a Tottenham Jan Vertonghen na da yaƙinin cewa tsohon kocinsa Mauricio Pochettino na duba yiwuwar sa ke komawa ƙulob ɗin Frimiya, idon sa na kan Manchester United. (Star)
Ɗan wasan da ke buga tsakiya a Arsenal Matteo Guendouzi mai shekara 21, ya bayyana cewa abokan wasansa Mesut Ozil da Bernd Leno sun Ƙarfafa masa gwiwar tafiya Hertha Berlin a matsayin ɗan aro. (Kicker via Goal)
Raunin da mai buga tsakiya a Liverpool Fabinho ya yi bai kai tsananin da aka yi tunani ba da farko. Ɗan asalin Brazil mai shekara 27, ba zai haska ba a wasanni uku gaba. (Mirror)
Juventus za ta ci gaba da rike kocinta Andre Pirlo, duk da sukar da take sha daga kafafan yaɗa labaran Italia kan yadda ta shiga kakar bana. (Mail)
Ɗan wasan gaba a Everton Theo Walcott, ya ce ya zaƙu ya yi aiki tare da kocin Southampton a kwantiragi na dindindin. Walcott mai shekara 31 na zaman aron a Saints. (Liverpool Echo)
Ryan Giggs, na ganin cewa Manchester United za ta iya shafe shekaru 15 zuwa 20 ba tare da ta yi nasarar lashe kofin Firimiyar Ingila ba. (Metro)
Kocin Chelsea Frank Lampard, ya ce bai taɓa nuna shakku kan Christian Pulisic na Amurka mai shekara 22 ba, a fagen Firimiya. (ESPN)
Mai buga tsakiya a Nertherlands Donny van de Beek, na iya koyi da Thomas Muller na Bayern Munich a Manchester United, a cewar tsohon ɗan wasan tsakiya Owen Hargreaves. (BT Sport, via Independent)