An Kuma: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mumunan Hari Jihar Zamfara, Sunyi Aika-Aika

Wasu yan bindiga a ranar Alhamis sun kai hari garin Gidan Goga dake karamar Maradun na jihar Zamfara, inda mutane da zama suka rasa rayukansu, cewar rahoton Daily Trust.

Mazauna sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun dira garin kan babura suna harbin mutane kafin sukayi awon gaba da shanu da awaki. Wani tsohon kwamishanan ilimin jihar Zamfara, wanda dan gari Gidan Goga ne, Ibrahim Danmalikin Gidan Goga, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindigan sun dira garin misalin karfe 1 na rana.

“An sanar da Sojoji kuma sun isa wajen da wuri kafin yan bindigan su tafi. An yi musayar wuta tsakanin Sojoji da yan bindigan,” yace “Ba zan iya fada maka adadin wadanda suka mutu yanzu ba amma ina da tabbacin mazauna garin sun arce daga muhallansu.” Ba’a samu jin ta bakin kakakin hukumar yan sanda jihar, SP Muhammad Shehu, ba yayin tattara wannan rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here