Dalilin da Yasa Wata Mata Take Son Kotu ta Raba Auranta
Wata matar aure ta nemi kotu ta raba aurensu da mijinta na tsawon shekaru 18 a garin Ibadan.
Matar mai suna Nafisat ta kafa hujjar cewa mijinta mafadaci ne kuma yana barazana ga rayuwarta ta hanyar murde mata wuya har sai da ta suma.
Alkalin kotun ya raba auren sannan ya mika wa mai karar ragamar kula da yayan da suka haifa su biyu.
Wata yar kasuwa, Nafisat Olajire, a ranar Litinin, ta shigar da kara wata kotun gargajiya da ke Ibadan domin a raba aurenta na shekaru 18 da mijinta, Sarafa Olajire, saboda yana yawan yunkurin murde mata wuya.
Matar mai yaya biyu wacce ke zama a Olunkemi-Olomi a Ibadan ta sanar da Cif Ademola Odunade, Shugaban kotun, cewa a baya mijinta ya taba makure mata wuya har sai da ta rasa inda kanta yake.
Ta ce sai da likitoci suka shiga lamarin kafin ta farfado, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
“Ya mai shari’a, ban samu kwanciyar hankali ba tsawon shekaru 18 da suka gabata a aurena da Sarafa saboda muguntarsa gareni ta hanyar yawan dukana da tozartani a idon jama’a.
“Har ta kai, ya kan so daukar raina ko a gaban wanene.
“Na karshen da yayi wanda shine ya kai ga har na shigar da wannan karar shine lokacin da ya makure mun wuya har sai da na suma.
“Wannan ba shine karon farko da Sarafa ke kokarin kashe ni ba, ya bugi kirji har a gaban iyayena cewa wata rana sai ya raba ni da duniya.
“Bugu da kari, baya mutunta ni sabod a yana yawan yi mun tsirara.
“Sarafa ya kan kuma yi farauta ta a gari, yana barazanar cewa zai yanka ni,” in ji Nafisat.
Sai dai kuma, wanda ake karar wanda ke aikin hura wa taya iska ya yi adawa da karar, amma kuma bai karyata yawancin zarge-zargen da ake masa ba.
Sarafa, wanda ke zama a yankin Olomi-Academy da ke Ibadan, ya bayyana cewa matarsa bata da biyayya kuma bata son daukar umurninsa.
Ya kuma mika ragamar kula da yaransu biyu ga matar.
Mai shari’an ya umurci Sarafa da ya biya N10,000 a matsayin kudin abincin yaran duk wata sannan kuma shi zai dauki nauyin karatunsu da sauransu.