Watford ta Kori Kocinta, Xisco Munoz
Watford ta kori mai horar da ita, Xisco Munoz, bayan wata 10 yana jan ragamar kungiyar.
Mai shekara 41, dan kasar Spaniya ya kai kungiyar gasar Premier League daga Champions League a bara, bayan da ya karbi aikin a cikin Disambar 2020.
Watford tana ta 14 a kasan teburi mai maki bakwai daga wasa bakwai a kakar bana, kuma Xisco ya ja ragamar wasansa na karshe ranar Asabar da Leeds ta yi nasara da ci 1-0 a gasar Premier League.
Shine kocin farko a babbar gasar Ingila da aka sallama daga aiki a bana, kuma na 13 da ya bar aikin tun bayan da iyalan Pozzo suka mallaki Watford a 2012.
Read Also:
Ana alakanta Claudio Raneiri, wanda ya ja ragamar Leicester City ta lashe Premier League a karon farko a tarihi a 2016 da cewar shine zai maye gurbin Xisco.
Watford ta fara kakar bana da kafar dama da cin Aston Villa 3-2 a wasan farko da bude gasar Premier League ta kakar nana.
Haka kuma Kungiyar ta cire Crystal Palace daga Carabao Cup a fafatawar zagaye na biyu.
Watford ta ci karo da koma baya ne, bayan cin wasa biyu daga karawa bakwai, sannan Stoke City ta yi waje da ita daga Carabao Cup da ci 3-1 a wasan zagaye na uku a cikin watan Satumba.
Watford za ta buga wasan mako na takwas a gasar Premier League da Liverpool ranar 16 ga watan Oktoba.