Kotu ta yi Watsi da Shari’ar Sirikin Atiku Abubakar
Wani alkali da ke zama a babban kotun tarayya da ke Legas ya yi watsi da shari’ar sirikin Atiku.
Alkalin ya bayyana cewa kotun bata da hurumin yanke hukunci saboda an yi laifin ne a Abeukuta.
Ana zargin Abdullahi Babalele, wanda sirikin Atiku ne da harkallar wasu kudi har $140,000.
Mai shari’a Chukwujekwu Aneke da ke zama a babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Litinin ya sallami Abdullahi Babalele, sirikin Atiku Abubakar, a kan zarginsa da ake da handamar kudi har $140,000.
Read Also:
Kotun ta yi watsi da karar da hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta shigar, sakamakon rashin hurumin kotun na sauraron shari’ar bisa ga duban yankin, Daily Trust ta wallafa.
Ya yanke hukuncin cewa, wannan karar da aka maka wanda ake zargin bai kamata a kai ta har jihar Legas ba domin ana zarginsa da aikatawa ne a garin Abeoukuta da ke jihar Ogun.
Alkalin ya dogara da hukuncin kotun koli a wata shari’a tsakanin EFCC da Mohammed Dele Belgore a kan irin haka.
An gurfanar da babalele a shekarar 2018 kuma aka sake gurfanar da shi a ranar 8 ga watan Oktoban 2019.
EFCC ta zargi Babalele da bai wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo $140,000 bisa umarnin Abubakar wanda ke neman kujerar shugaban kasa a 2019.
Ya musanta aikata abinda ake zarginsa da shi a dukkan zaman da aka yi a kotun.