Wike ya Kasa Kaɗa ƙuri’arsa

 

Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya gaza kaɗa ƙuri’arsa saboda kalubalen na’urar Bvas mai tantance masu kaɗa ƙuri’a.

Masu aikin zaɓen daga INEC sun shawarce shi da ya koma gida daga baya sai ya je ya yi zaɓen, yayin da su kuma suka kira masu gyara na’urar.

Gwamnan ya je wurin ne tare da matarsa Justice Eberechi Suzzette Nyesom-Wike, domin kaɗa ƙuri’ar tasa a mazaɓar Rumuepirikom da ke ƙaramar hukumar Obio Akpor.

Ya nuna rashin jin daɗinsa game da wannan na’ura da ke tantance mutum da ɗan yatsa ko kuma da fuska, game da yadda ta gaza aiki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here