Gwamna Nyesom Wike ya Mayar da Martani Kan Kalubalen da Rochas Okorocha ya Fuskanta

 

Gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya mayar da martani game da kalubalen da Sanata Okorocha ya fuskanta kwanan nan.

Wike ya shawarci dan majalisar kan yadda zai magance matsalolin siyasarsa.

Kwanan nan ne hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta tsare Okorocha na tsawon awanni 48 kafin aka ba shi beli Gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya fice daga gidan gwamnati a shirye-shiryen barin ofis idan wa’adin mulkinsa ya kare a 2023.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Wike ya bayyana hakan ne a wajen taron sunan wani yaro a Abuja, cewa ya san wasu tawagar siyasa za su biyo shi bayan ya bar mulki.

Ya ce a shirye yake ya fuskanci irin wadannan matsalolin lokacin da ya sauka daga mukaminsa na gwamna.

Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu Sanata Okorocha da danginsa suna cikin tsanantawa ta siyasa.

Ya shawarci sanatan da ya jajirce domin zai fita daga matsalolin da karfinsa, jaridar The Sun ta ruwaito.

Wike ya ce:

“Mahukuntan siyasa za su bibiye ka musamman bayan ka bar ofis saboda haka abin da kake fuskanta a yau ba sabon abu bane kan ka da iyalanka. Na san za su bibiyeni amma na shirya, na shirya masu.”

Sanata Rochas Okorocha ya yi magana game da yanayin da ya sa aka sake shi daga hannun hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here