Takaitaccen Tarihin Rayuwar Idriss Deby 

 

A makon nan ne ake jimamin mutuwar Idriss Déby Itno. Kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban Chad, wanda ya shafe sama da shekara 30 a mulki.

Legit.ng Hausa ta tsakuro wasu bayanai a kan tarihin rayuwar Idriss Déby Itno daga shafin Britanica.

1. Haihuwa

An haifi Idriss Déby Itno a shekarar 1952 a wani gari da ake kira Fada a kasar Chadi. Marigayi Idriss Déby Itno ya mutu ya na mai shekara 68. Deby ya na cikin mutanen kabilar the Zaghawa da su ke yankin Ennedi a Arewacin kasar Chadi.

2. Karatu

A farkon shekarun 1970 ne Idriss Déby ya shiga gidan soja, a wancan lokaci kasarsa ta na cikin yakin basasa.

A 1976 ya tafi kasar Faransa ya yi karatun iya tuka jirgin sama.

3. Shiga siyasa

Bayan dawowarsa gida a 1978, ya mara wa shugaban dakarun ‘yan taware, Hissène Habré baya. A karshe Habré ya yi nasarar karbe mulki a 1982, ya zama shugaban Chadi.

4. Suna Marigayin ya samu shahara a sakamakon juyin mulkin Hissène Habré, daga nan aka nada shi a matsayin shugaban hafsun soja, ya kuma tafi kasar Faransa ya kara karatu.

5. Juyin-mulki

A farkon 1989 aka soma zargin Déby da shirin kifar da gwamnatin Habré, wannan ya sa ya tsere zuwa Sudan.

Daga Darfur, Déby ya shirya rundunar da ta kifar da gwamnati.

6. Shugaban kasan Soji

Bayan ya yi nasarar hambarar da Hissène Habré a 1990, Idris Déby ya dare kan mulki, ya dakatar da tsarin mulki.

Déby ya yi alkawarin gyara kasar da kuma dawo da siyasa.

7. …Ya rikida A wani taron kasa da aka yi a 1993 sai Déby ya zama shugaban kasa na rikon kwarya. A shekarar 1996 aka tsara sabon kundin tsarin mulki, kuma ya shiga zabe, ya yi nasara.

8. Tazarce Duk da koke-koken jama’a, Déby ya cigaba da zama a kan mulki, ya na lashe duka zabukan da aka gudanar a 2011, 2006, 2011 har zuwa zaben da aka yi a shekarar nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here