Ya yi Wuri da za a Fara Kira ga Shugabancin Igbo a 2023 – Gwamna David Umahi

 

Gwamna Dave Umahi ya sake yin Allah wadai da jerin tattaunawar da ake yi game da zabubbukan 2023 a kasar.

Gwamnan jahar Ebonyi ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Umahi ya bayyana cewa ya yi wuri da za a fara irin wannan tattaunawar har ma da jan hankali sosai, inda ya bukaci takwarorinsa da su mai da hankali kan abubuwan ci

Ebonyi – Yayin da yakin neman zaben shugaban kasa ke kara ta’azzara a kowace rana, gwamnan jahar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce ya yi wuri da yawa da za a fara kira ga shugabancin Igbo a 2023.

Leadership ta rawaito cewa ya yi wannan bayanin ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba a fadar shugaban kasa.

Umahi ya shawarci gwamnonin kudu maso gabas da gwamnonin APC da su mayar da hankali kan ayyukan da za su kawo ci gaba a jaharsu, yankinsu da ma kasa baki daya.

Ya ce:

“To, a gare ni, Na fi zurfafa ga kammala ayyukana. Kuma zan duba harkokin siyasa lokacin da wa’adin mulki na ya cika shekara daya, wanda zai kasance daga ranar 29 ga Mayu, 2022. Kuma ina tsammanin hakan yake ga sauran gwamnonin Kudu maso Gabas da gwamnonin APC.”

Idan za a iya tunawa Gwamna David Umahi ya ce ana bukatar zabin Allah don Igbo su samar da shugaban Najeriya a 2023, Premiumtimes ta kuma rawaito.

Ya kara da cewa an kara samun kiraye-kiraye kan wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari ya fito daga Kudu maso Gabashin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here