Magance Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari ya Dira Jahar Imo

 

Shugaba Buhari yayi alkawarin taimakawa gwamnan Imo wajen ayyuka da tsaro.

Buhari ya kaddamar da manyan ayyukan da gwamnan yayi a jahar.

Imo – Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya yi alkawarin taimakawa gwamnan jahar imo, Hope Uzodinma, wajen kawo cigaba jaharsa ta hanyar samar da ayyuka.

Hakazalika Buhari ya bada tabbacin cewa zai yi amfani da ikonsa wajen taya gwamnan magance matsalar tsaro.

Buhari, wanda yayi magana yayin kaddamar da titin Egbeada-Onitsha a Owerri, yace ya gamsu gaskiya a ayyukan da gwamnan yayi, rahoton Punch.

Yace babu al’ummar da zata samu cigaba idan babu ayyukan jin dadin al’umma da tsaro.

A cewarsa:

“Na zagaya kuma na gamsu da abubuwan da na gani. Duk al’ummar da ba tada tsaro da ayyukan jin dadi ba zata cigaba ba, kuma ana ra’ayi na ya hadu da na gwamnan jahar Imo.”

“Zan yi amfani da karfi na kundin tsarin mulki ta bani wajen taya gwamna yin nasara.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Owerri, jahar Imo

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Owerri, babbar birnin jahar Imo da safiyar Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Buhari ya amsa gayyatar da gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma, yayi masa domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta kammala.

Daga cikin wadanda suka tarbi shugaba Buhari akwai gwamnan jahar Ebonyi da manyan jami’an gwamnatin jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here