Hukumar NDLEA ta Kama Miyagun Kwayoyi Masu Kimar N6b a Jahar Legas

 

Shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA, Buba Marwa ya bayyana yadda suka kwace miyagun kwayoyi masu kimar naira biliyan 6.

A ranar Laraba yayin wani taro, ya bayyana yadda suka kama miyagun kwayoyi a filin jirgin ruwa da ke Apapa, jahar Legas wanda aka turo daga gabas ta tsakiya.

A cewar sa, miyagun kwayoyin masu suna Captagon suna da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke gabas ta tsakiya kuma NDLEA ta samu bayanan sirri kan su.

Lagos – Shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana yadda suka kwace miyagun kwayoyi masu kimar naira biliyan 6 a filin jirgin ruwa da ke Apapa, jahar Legas.

TheCable ta rawaito cewa, ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba inda shugaban NDLEA din ya ce kwayoyin sun zo ne daga gabas ta tsakiya.

A cewarsa, hukumar ta samu bayanan sirri ne daga abokan huldar ta dangane da safarar kwayoyi ta filin jirgin Apapa.

Marwa ya ce kwayoyin masu suna Captagon suna da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda da ke gabas ta tsakiya, TheCable ta rawaito.

“A watan Maris din 2021, mun samu bayanan sirri daga abokan huldar mu na batun safarar miyagun kwayoyi a Najeriya daga gabas ta tsakiya ta filin jirgin kasa na Apapa.

“Kayan sun wuce ta kasashe 3 sannan suka iso kasar arewacin Afirka amma muka cigaba ta bin kayan,” kamar yadda takardar ta zo wacce Femi Babafemi ya saki.

“A ranar Alhamis 26 ga wata. Augusta muka fara bi takan kayan inda muka ga wasu injinan gyara gilasai da sauran su.

“A ranar Litinin 31 ga watan Augusta muka ci gaba da bincike ta hanyar anfani da karen mu, sai muka gane kayan suna cikin daya daga cikin injinan.

Washegari, 1 ga watan Satumba muka ga kwayoyin Captagon 18,560 masu nauyin 3.2kg da aka boye a wayoyin injin din.

A ranar 2 ga watan Satumba, mun sake bude ijinan 2 kuma mun samu kwayoyi 451, 807 masu nauyin 74.119Kg a cikin kwayel din.

Idan muka duba darajarsu a gari, kowacce kwaya ana siyar da ita kan dala 25. Mai su zai iya siyar da su kan dala miliyan 11.3 daidai da biliyan shida.

Buba Marwa ya kara da bayyana cewa, wannan ne karo na farko da aka taba shigowa da kwayar wata kasar Afrika kuma an yi hakan ne saboda ‘yan ta’adda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here