A Shirye Muke Don Kwace Mulki Daga Hannun APC a Zaɓen 2023 – Gwamnonin PDP

 

Gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko karkashin PDP sun bayyana shirin da suke na kwace mulki daga hannun APC.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal, yace yanzun kansu a haɗe yake kuma zasu ceto Najeriya daga APC.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnonin sun shafe awanni 7 suna tattaunawa kan rikicin dake faruwa a cikin PDP.

Abuja – Gwamnonin PDP sun bayyana cewa zasu haɗa kan jam’iyyar su domin ceto Najeriya daga hannun gurbatacciyar gwamnatin APC a zaben 2023, kamar yadda the cable ta rawaito.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba da daddare, jim kaɗan bayan taron da suka gudanar a Abuja.

Yace taron wanda ya gudana a sirrince sun cimma nasara, inda suka tattauna kan gangamin taron PDP na ƙasa dake tafe.

Guardian ta rawaito Tambuwal yace:

“Mun jima muna gudanar da taron, tun ƙarfe 3:00 na yamma, kuma sai da muka shafe awanni 7 muna tattaunawa.”

“Mun gana da shugabannin PDP na jahohin da bamu da gwamna, mun tattauna da su kan yadda zamu kawo cigaba a cikin PDP, ba wai a babban gangami kaɗai ba, har zuwa gaba.”

“Saboda PDP ta cigaba da samun nasara a Najeriya, kuma mu aike da sako mai kyau ga yan Najeriya cewa mun shirya, mun zama tsintsiya ɗaya.”

“Kuma da izinin Allah zaɓen 2023 dake tafe, zamu haɗa karfi da karfe domin ceto Najeriya daga gurɓatacciyar gwamnatin jam’iyyar APC.”

Waɗanne abubuwa aka tattauna a wurin taron?

Gwamna Tambuwal yace gwamnonin sun tattauna game da babban taron jam’iyyar PDP na ƙasa, wanda aka saka za’a gudanar ranar 20 ga watan Oktoba.

“Zaku ji matakan da zamu ɗauka kan gangamin a taron kwamitin zartarwa (NEC) da za’a yi gobe.”

Kwamitin NEC na jam’iyyar PDP zai gudanar da taro ranar Alhamis domin tattauna kan rarraba manyan mukaman jam’iyyar zuwa yankunan kasar nan yayin da gangami na kasa ke kara kusantowa.

Zaɓen gwamnan Anambra

Da yake jawabi, Tambuwal yace gwamnoni da sauran shugabannin jam’iyya sun tattauna kan shirye-shiryen PDP a zaɓen gwamnan Anambra.

“Ɗan takarar mu a zaben Anambra ya samu halarta, kuma mun ji bayanai daga bakinsa kan shirye-shiryen PDP a Anambra, kuma muna tabbatar muku da cewa baki ɗayan mu kan mu a haɗe yake wajen goyon bayan jam’iyyar mu a Anambra.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here