‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Matafiya 5 a Jahar Ondo

 

‘Yan bindiga sun kai farmaki kan wata motar haya da ke dauke da fasinjoji 18 a kan babbar hanyar Ido Ani-Ifira, jahar Ondo.

Maharan sun yi garkuwa da mutane biyar a yayin harin wanda ya afku a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba.

Shugaban ‘yan sandan da ke kula da sashen rundunar na Isua Akoko, Mista Hakeem Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata motar kasuwa da ke dauke da fasinjoji 18 a kan babbar hanyar Ido Ani-Ifira, jahar Ondo a yammacin ranar Laraba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa motar na a hanyar zuwa Abuja daga jahar Legas lokacin da aka kai masu harin.

Rahoton ya ce ‘yan bindigar sun ja wadanda abin ya shafa cikin daji zuwa inda ba a sani ba.

Shugaban ‘yan sandan da ke kula da sashen rundunar na Isua Akoko, Mista Hakeem Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kai rahoton lamarin, inda ya kara da cewa sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar da sauran hukumomin tsaro suna aiki tukuru don kubutar da matafiyan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here