Rigakafin Corona: Gwamnatin Tarayya ta Yabawa Shugabannin CAN Bisa Goyan Bayan da ta Basu
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta fara kai allurar riga-kafin corona zuwa coci a Najeriya.
Ta kuma yabawa wasu shugabannin CAN bisa goyon bayan da suka bayar na yin allurar a coci.
Hakazalika, ga mambobin coci, gwamnati ta yaba musu wajen ba ta hadin kai don cimma burin yin riga-kafin.
Abuja – Gwamnatin tarayya a ranar Talata 14 ga watan Satumba ta sanar da shirinta na daukar allurar riga-kafin corona zuwa cibiyoyin bauta ta Kiristoci, Punch ta rawaito.
Read Also:
Babban Darakta na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan ne yayin wayar da kan shugabannin Kiristoci kan kashi na biyu na riga-kafin corona a babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce:
“Mai martaba, Shugaban CAN, fitattun shugabannin Kirista, mata da maza, ina mai farin cikin sanar da ku cewa daga wannan mataki na 2 na riga-kafin corona, mun gabatar da allurar riga-kafin ranar Lahadi.
“An yi wannan ne don tabbatar da membobin Kiristoci da watakila ba su sami damar yin allurar riga-kafi ba saboda wani dalili an ba su damar yin allurar riga-kafin a wuraren bautarsu.
“Dole ne in fadi cewa sakamako daga coci yana da kyau sosai kuma ina godiya ga dukkan shugabannin Kiristocin da suka ba kungiyar allurar riga-kafin damar zuwa majami’un su da membobin su don samun allurar corona yayin bautar ranar Lahadi.