Hukumar EFCC ta Bayyana Yadda Tsohon AGF, Ahmed Idris ya karɓi Cin Hancin N15bn
Abuja – Acanta Janar na ƙasa (AGF) da aka dakatar, Ahmed Idris, ya karɓi biliyan N15bn ta bayan fage domin ya gaggauta biyan jihohi masu fitar da ɗanyen mai kason su.
Hukumar yaƙi da masu yi ea tattalin arziƙin ƙasa ta’adi (EFCC) ta ce dakataccen AGF ɗin ya karɓi kudin ne a matsayin toshiyar baki domin saurin tura wa jihohin guda 9 ƙaso 13% da ake ware musu.
Daily Trust ta ruwaito cewa ƙaso 13% na kuɗaɗen da aka samu wata garabasa ce da tsarin rabo ya ware domin taimaka wa yankun da ake haƙo ɗanyen mai su cigaba.
Read Also:
Kuɗaɗen na zuwa ne daga asusun tattara kuɗin shiga na tarayya zuwa yankunaɓ ta hannun gwamnatocin jihohin su kamar yadda yake a sashi na 162 ƙarashin sashi na 2 a kundin mulkin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa johohi 9 da ke fitar da ɗanyen man fetur a Najeriya sun kasafta Biliyan N450.60bn daga asusun tarayya ya hanyar kaso 13%da ake ware musu a 2021.
Jihohin da ke shan wannan romon demokaraɗiyya sune: Delta, Akwa Ibom, Bayelsa, Ribas, Edo, Ondo, Imo, Legas da kuma Abia.
Yadda AGF ya karɓi cin hancin kuɗin
A cewar hukumar EFCC, Idris ya karɓi tukuicin N15,136,221,921.46 daga wurin Olusegun Akindele, domin ya taimaka wajen gaggauta tura wa jihohin kaso 13% da ake ware musu.
Akindele ya kasance mai taimaka wa AGF ta ɓangaren fasaha daga watan Fabrairu zuwa Nuwamba na shekarar 2021.
AGF Idris zai gurfana gaban mai shari’a A.O. Adeyemi Ajayi, na babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ranar Jumu’a, 22 ga watan Yuli.