Sadio Mane ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Afirka na 2022
Sabon dan wasan Bayern Munich Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022.
Karo na biyu kenan da dan kwallon tawagar Senegal ya lashe kyautar, bayan da ya dauka a 2019 daga nan ba a gudanar da bikin ba, saboda cutar corona.
Tsohon dan wasan Liverpool ya yi takara tare da Edouard Mendy dan wasan Senegal da Chelsea da kuma Mohamed Salah na Masar da Liverpool.
Kyaututtukan da aka lashe a bikin karrama ‘yan kwallon Afirka na 2022
Masu takarar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022
Wanda ya lashe kyautar: Sadio Mane na Senegal da Bayern Munich
Wadanda suka yi takara:
Edouard Mendy na Senegal da Chelsea
Mohamed Salah na Masr da Liverpool
Matan da ke takarar gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 2022
Wadda ta ci kyautar: Asisat Oshoala ta Najeriya da Barcelona
Wadanda ta yi takara da su:
Ajara Nchout Njoya ta Kamaru da Inter Milan
Grace Chanda ta Zambia da BIIK Kazygurt)
Matan da ke takara masu taka leda a Afirka da ba kamarta
Wadda ta ci kyautar: Evelyn Badu ta Ghana da Sekondi Hasaacas Ladies/Alvaldsnes)
Wadanda suka yi takara:
Andile Dlamini (South Africa & Mamelodi Sundowns)
Bambanani Mbanie (South Africa & Mamelodi Sundowns)
Mazan da ke takara masu buga kwallo a Afirka da ba kamarsa
Wanda ya zama zakara: Mohamed El Shenawy (Masar da Al Ahly)
Wadanda ya yi takara da su:
Achraf Dari (Morocco & Wydad Athletic Club)
Aliou Dieng (Mali & Al Ahly)
Matashiyar ‘yar kwallon kafa ta Afirka
Read Also:
Wadda ta lashe kyautar: Evelyn Badu (Ghana da Sekondi Hasaacas Ladies/Alvaldsnes)
Wadanda ta yi Takara da su:
Doris Boaduwaa (Ghana & Sekondi Hasaacas Ladies)
Yasmine Zouhir (Morocco & AS Saint-Etienne)
Masu takarar matashin da ba kamarsa a Afirka
Wanda ya lashe kyautar: Pape Matar Sarr (Senegal & Tottenham Hotspur)
Wadanda ya yi takara da su:
Hannibal Mejbri (Tunisia & Manchester United)
Karim Konate (Cote d’Ivoire & ASEC/RB Salzburg)
Koci mace da ke takara a 2022
Wadda ta lashe kyautar: Desiree Ellis ta Afirka ta Kudu
Wadanda ta yi takara da su:
Bruce Mwape Zambia
Jerry Tshabalala Mamelodi Sundowns)
Reynald Pedros Morocco
Koci namji da yafi kowa yin fice a 2022
Wanda ya karbi kyautar: Aliou Cisse kociyan Senegal
Wadanda suka yi takara:
Carlos Queiroz na Masar
Walid Regragui na Wydad Athletic Club
Kungiyar kwallon kafa ta mata a Afirka da ta taka rawar gani
Wadda ta lashe kyautar: Mamelodi Sundowns (South Africa)
Wadanda suka yi Takara:
AS FAR (Morocco)
Hasaacas Ladies (Ghana)
Kungiyar maza da ba kamarta a tamaula a Afirka
Wadda ta lashe kyautar: Wydad Athletic Club (Morocco)
Wadanda suka yi Takara:
Al Ahly (Egypt)
RS Berkane (Morocco)
Tawaga ta maza da ke kan gaba a Afirka
Wadda ta lashe kyautar: Senegal
Wadanda suka yi Takara tare:
Kamaru
Masar
Kwallon da aka zura a raga mafi kayatarwa
Wanda ya lashe kyautar: Pape Ousmane Sakho (Senegal & Simba)
Wadanda suka yi takara:
Gabadinho Mhango (Malawi & Orlando Pirates)
Zouhair El Moutaraji (Morocco & Wydad Athletic Club)