Yaduwar Covid-19: ‘Yan Bautar Kasa 100 Sun Kamu da Cutar

 

Akwai ‘yan bautar kasa sama da 100 da aka samu dauke da COVID-19.

Hukumar NYSC ta wajabta yin gwaji idan an shiga sansanin bada horo.

Yaduwar Coronavirus ta fi kamari a jahohin Sokoto, Edo, Taraba, Filato.

Najeriya – Hukumar NYSC ta shiga damu wa yayin da aka samu akalla matasa 109 da ke yi wa kasa hidima a halin yanzu da suke dauke da cutar COVID-19.

A karshen makon da ya gabata ne aka bude sansanin horas da ‘yan bautar kasa.

A cikin sahun masu hidimar, an samu sama da matasa 100 dake da COVID-19.

Daily Trust ta ce hukumar NYSC ta gano hakan ne a sakamakon wajabta yin gwajin cutar da aka yi.

Alkaluman COVID-19 a jahohi A jahar Edo, masu bautar kasa 17 aka samu da COVID-19 a lokacin da aka bude sansanin horaswar kamar yadda shugabar NYSC, Abiodun Olubukola, ta bayyana.

Haka zalika a sansanin NYSC da ke garin Mangun jahar Filato, an samu mutane 26 daga karshen makon jiya zuwa jiya, da aka tabbatar da Coronavirus ta harba.

Shugabar NYSC ta jahar Gombe, Ada Imoni ta kafa wani kwamiti na musamman da zai yi yaki da COVID-19 bayan an gano matasa har 25 sun kamu da COVID-19.

A Sokoto akwai ‘yan bautar kasa 14 da aka samu su na dauke da COVID-19. Kwamishinan lafiya na jahar Sokoto Dr. Ali Inname, ya shaida wa ‘yan jarida wannan.

Abin mamaki babu wani ‘dan bautar kasa da aka samu da cutar a Legas, amma an samu COVID-19 ta harbi matasa 21 a Taraba, da kuma mutane shida a jahar Ogun.

A Neja akwai mutane 18 daga cikin wadanda aka tura zuwa jahar domin su yi wa kasa hidima da aka samu da cutar inji kwamishinan labarai, Muhammed S. Idris.

Wadanda suka kamu da COVID-19 sun kara yawa Alkaluman hukumar NCDC sun nuna ana samun karuwar masu dauke da wannan cuta.

Mutane 851 aka samu da COVID-19 a kwanakin farko na Agustan nan.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke cewa ayi hattara da samfurin Coronavirus wanda ya shigo Najeriya, kuma ya na kama mutane.

Rahotanni sun ce mutum 32 sun kamu da sabon samufurin COVID-19, don haka kwamitin PSC ya ware Jahar Akwa Ibom, ya ce annobar ta fi kamari a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here