Najeriya Na Bukatar Sama da Tiriliyan Guda Domin Yaki da Zazzabin Cizon Sauro – Ministan Lafiya

 

Ministan lafiya a Najeriya bayyana bukatar makudan kudade don yaki da zazzabin cizon sauro.

Ministan ya yarda kasar ba ta isassun kudade duba da yadda annobar Korona ta lalata tattalin arziki.

Ya kirayi kungiyoyi da su tallafawa gwamnati wajen yaki da zazzabin na cizon sauro a kasar.

Najeriya na bukatar sama da naira tiriliyan guda domin yaki da zazzabin cizon sauro a kasar, in ji Dokta Osagie Ehanire, gidan Talabijin na Channels ta ruwaito.

Ya bayyana cewa daga cikin jimillar kudin, kasar na bukatar sama da naira biliyan 350 don yaki da cutar a shekarar 2021 kadai. Ehanire, Ministan Lafiya, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

“Aiwatar da sabon tsarin zai ci naira tiriliyan 1.89; ana bukatar kimanin Naira biliyan 352 don aiwatar da shirin a shekarar 2021,” ya shaida wa manema labarai haka ne gabanin ranar zazzabin cizon sauro ta Duniya da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi.

Ya yarda cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da isassun kudin da ake bukata don yaki da cutar a bana. Ehanire ya danganta hakan ne ga yanayin tattalin arzikin da ake fama da shi a sanadiyyar annobar Korona, kamar dai yadda yake a wasu kasashe.

Don haka, ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyi daban-daban, da masu kishin kasa da su ba gwamnati goyon baya don magance zazzabin cizon sauro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here