‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyaya 3 a Jahar Kaduna
Daga jahar Kaduna, an hallaka wasu makiyaya a wani harin ramuwar gayya da aka kai wani kauye.
Rahoto ya bayyana cewa, akalla mutane uku ne suka mutu, sannan wasu da dama sun jikkata.
Rahoton ya fito ne daga ofishin kwamishinan tsaron cikin gida na jahar kaduna, Samuel Aruwa.
Kaduna – Rahotanni sun ce an kashe wasu makiyaya uku a wani harin ramuwar gayya da wasu ‘yan bindiga suka kai wa Ribok, Tsoriyang da Kankada da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jahar Kaduna.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi 22 ga watan Agusta, Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jahar Kaduna, ya ce harin na ramuwar gayya ne a kauyen Ungwan Dooh na karamar hukumar, The Cable ta rawaito.
Ya ce ‘yan bindigar sun nufi harin ga gidan wani mutum ne Ardo Tanko Usman, inda mutane uku da ke cikin gidan aka hallaka su.
Wadanda aka kashe din sun hada da Bayero Wake, Isah Usman da Abu Usman.
A sanarwar, Aruwan ya ce:
“Mazauna hudu sun ji rauni. Su ne Ambo Jamo, Sule Ambo, Muazu Ori da Ibrahim Mohammed.”
“An kone tare da lalata mota daya, gidaje uku da bukkokin makiyaya takwas. Sojoji da ‘yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru tare da kwashe makiyaya da yawa domin kare lafiyarsu.
“Ana ci gaba da ayyukan bincike da ceto kuma za a ba mazauna labarin duk wani ci gaba da aka samu.
“Mukaddashiyar gwamna Dr Hadiza Balarabe ta karbi rahoton cikin bacin rai tare da yin tir da yadda ake kashe-kashe da ramuwar gayya a yankin.
 “Ta yi addu’ar Allah ya jikan mamatan sannan ta aika da ta’aziyya ga iyalansu. Ta kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. ”
Kwamishinan ya ce gwamnatin jahar ta yi kira da a kwantar da hankula sannan ta bukaci mazauna yankin da su guji daukar doka a hannu yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here