Ya Kamata Gwamnatin Tarayya ta yi Taka Tsantsan Gurin Yafewa Tubabbun Boko Haram – Rev.Ignatius Kaigama

 

Wani babban malamin coci a Abuja ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan saurin amincewa da tubabbun ‘yan Boko Haram.

Rabaran Kaigama yace za’a iya yafewa yan ta’addan da suka tuba amma ya kamata gwamnati ta yi taka tsantsan.

A cewarsa duba da abinda ya faru a kasar Afghanistan na kwace iko, ya kamata a yi adalci.

Abuja – Wani babban malamin coci a Abuja, Rev. Ignatius Kaigama, ya gargaɗi gwamnatin tarayya game da yin gaggawar amincewa da tubabbun yan Boko Haram, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Malamin yace za’a iya yafe wa yan Boko Haram ɗin amma ya kamata gwamnati ta yi adalci duba da yananyin da kasa ke ciki.

Kaigama yace:

“Ba zamu taɓa manta wa da abinda yan Boko Haram suka yi na kashe dubbannin mutane da jikkata wasu ba musamman a yankin arewa maso gabas.”

Wajibi gwamnati ta yi taka-tsantsan

Malamin cocin yace babban misalin da ya kamata gwamnati ta kalla shine abinda ya faru a ƙasar Afghanistan tsakanin gwamnati da Taliban.

“Misali mafi kusa kan hatsarin mika makamai da yan Boko Haram ke yi, da abinda zai haifar idan ba’a yi taka tsantsan ba shine abinda ya faru a ƙasar Afghanistan.”

“Inda yan kungiyar Taliban suka kwace mulkin kasar bayan janyewar sojojin kasar Amurka.”

Kaigama ya kuma yi gargadin cewa kada a yi kuskuren sa son rai a shirin canza wa tubabbun yan ta’addan tunani domin su koma rayuwa kamar kowa.

Ya kara da cewa gwamnati ta kula da jin daɗi da walwalar jami’an da zasu gudanar da wannan shirin domin kada a maida abun tamkar kasuwanci.

Kungiyoyin addinai su yi adalci

Malmain ya yi kira ga kungoyoyin addinai kamar MURIC, CAN, JNI da su daina saka son rai a wajen kokarin kare waɗanda suke inuwa ɗaya.

A cewarsa abinda suke yi na kakkausan raddi da nuna wa juna yatsa sam bai dace ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here