Wanda Sukai Garkuwa da ‘Yan Gida Daya Sun Bukaci N30m
Masu garkuwa da mutanen da sukayi awon gaba da mutane biyar yan gida daya a unguwar Pengi na garin Kuje a birnin tarayya Abuja sun ce wajibi ne a biyasu N30 million kudin fansa kafin su sakesu.
Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an sace wasu ƴan gida ɗaya su biyar a garin Pegi da ke ƙaramar hukumar Kuje a Abuja.
A cewar rahoton, wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Jubril Abdullateef (22), Sherifat Abdullateef (20), Muyidat Abdullateef (13) Nura Abdullahi (18) da Nahimat Abdullahi (9).
Read Also:
Wani dan’uwan wadanda aka sace, wanda aka sakaye sunansa, ya ce sun samu nasarar tattaunawa da masu satan mutanen lokacin da suka kira domin bukatan kudin fansa.
A cewarsa, masu garkuwan sun yi amfani da wayar hannun da suka kwace daga hannun mahaifiyar yara 5 da suka sace, Latifat Abdullateef, wajen kiransu.
“Iyalin sun samu nasarar tattaunawa da masu garkuwa da mutanen da yammacin Laraba, kuma sun bukaci milyan 30 kafin su sakesu, amma har yanzu ana tattaunawa, ” yace.
Kakakin hukumar yan sanda birnin tarayya, ASP Maryam Yusuf, ba ta daga wayarta ko amsa sakonninta ba domin tabbatar da gaskiyar bukatar masu garkuwan.