Gwamnatin Tarayya Tana Kokarin Raba Wani Attajiri da Kadarorinsa

Gwamnatin Tarayya ta fara raba Jimoh Ibrahim da wasu kadarorinsa.

An dauki wannan matakin ne bayan ‘dan kasuwar ya gaza biyan bashi.

AMCON ta ce ana bin Jimoh Ibrahim bashi na kusan Naira biliyan 70 Hukumar AMCON mai alhakin kula da kadarorin Najeriya, ta ce ta karbe wasu dukiyoyi da ‘dan kasuwar nan, Jimoh Ibrahim ya mallaka.

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, gwamnati ta karbe kadarorin gawurtaccen attajirin ne saboda tarin bashin da ke kansa.

Rahotanni sun bayyana cewa bashin da ke kan Mista Jimoh Ibrahim ya haura Naira biliyan 69.4.

A halin yanzu ana rufe duk wasu asusun banki da ke dauke da sunan Jimoh Ibrahim da kamfanoninsa; Global Fleet Oil & Gas Limited.

Hukumar AMCON ta ce ba ta kyale kamfanin ‘dan kasuwar na NICON Investment Limited ba. Pinheiro Legal Partners a madadin AMCON ya yi nasarar karbe kamfanin NICON Investment da ake da su a garuruwan Legas, Abuja da Fatakwal.

Bayan haka an rufe ofisoshin kamfanin International Hotels Limited da ke Legas da wani ginin tsohon bankin Allied Bank duk a garin na Legas.

Jaridar ta ce an rufe katafaren otel dinnan na NICON a Maitama da Garki a birnin tarayya Abuja.

Alkali R.M Aikawa na babban kotun tarayya a Legas ne ya hallata wa AMCON karbe kadarorin ‘dan kasuwar da aka san da su saboda kin biyan bashi.

Mai magana da yawun bakin AMCON, Jude Nwauzor, ya ce sun yi nasarar raba ‘dan kasuwar da dukiyoyinsa, bayan sun samu hadin-kan ‘yan sanda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here