Abubuwan Dana Fuskanta a Fadar Shugaban Kasa – Diyar Buba Galadima

Diyar tsohon makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ta koka da gwamnatin Buhari.

Ta bayyana yadda ta yi aiki na tsawon lokaci a fadar shugaban kasan amma ba a taba biyanta ba kuma ga wulakanci da take fuskanta.

Zainab ta ce a wani bangare kuma jama’a suna kallon cewa ana gwangwajeta ne da ababen arziki a rayuwa Zainab Buba galadima, diyar makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a da, Buba Galadima, ta ce har a halin yanzu mahaifinta dan jam’iyyar APC ne.

Kamar yadda Zainab, wacce tsohuwar jami’a ce a fadar shugaban kasa, ta ce akwai bukatar gyara a gwamnatin Buhari a irin abubuwan da ta gani.Ta ce in dai aiki a fadar ne, toh a kai kasuwa.

“Na dandana kuda ta saboda gani-gani da wasu suka dinga min yayin da nake aiki a fadar shugaban kasan. Akwai masu min bakar magana, babu wanda ban gani ba,” ta ce saboda sabanin mahaifinta da Buhari.

A wata hira da Aminiya Daily Trust ta yi da diyar Buban, ta ce shakarunta hudu tana aiki a fadar shugaban kasan amma ba a biyanta albashi. Duk yadda ta so a bata hakkinta, ya gagara.

Zainab wacce Buhari ne madaurin aurenta, ta ce, “A gaskiya ni ban yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa ba don a biya ni.”

“Na yi kokari mai yawa amma mutanen da ke kusa da Buhari kullum ba su gani. Daga nan ne na hakura kawai da aikin.”

“A wani bangare kuma ana nuna cewa gwanati ta rungumeni ana min sha tara ta arziki, amma ba hakan bane.” tace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here