‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Dake Tsaron Gidan Wani Tsohon Gwamna

Wasu yan bindiga sun halaka wani jami’in dan sanda ta hanyar harbinsa a harin da suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson.

Lamarin ya afku ne a daren jiya Laraba, 18 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Toru-Orua a karamar hukumar Sagbama, Bayelsa.

Dan sandan ya kasance daya daga cikin tawagar tsaro na musamman da ke gadin gidan tsohon gwamnan.

Yan bindiga sun harbe wani jami’in dan sanda har lahira a wani harin tsakar dare da suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da ke Toru-Orua a karamar hukumar Sagbama da ke jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai farmaki gidan Dickson ta kogin Forcados a daren ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.

Jami’in tsaron da aka kashe ya kasance daya daga cikin wata tawagar yan sanda na musamman da ke tsaron gidan tsohon gwamnan.

An tattaro cewa ya mutu ne a nan take. Da aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, ya ce zai koro jawabi a kan lamarin a nan gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here